Kisan gillar da ake yiwa al'ummar garin Gwoza ya shiga kwanaki na biyar lamarin da ya haddasa mutanen suka yi dafifi a gaban gidan gwamnan jihar Borno.
Da can an shirya gudanar da taron manema labarai a filin polo dake garin Maiduguri amma daga bisani kwamishanan 'yansandan jihar Lawal Tanko ya bada umurnin hana taron sabili da dalilan tsaro. Sabili da haka mutanen suka yi tattaki zuwa kofar fadan gwamnatin jihar dake birnin Maiduguri.
Ganin haka ya sa jam'an tsaro suka soma anfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa jama'ar. Ana cikin haka ne sai wani dansanda ya harbi wani mai suna Bello. To saidai mutumin bai mutu ba. Yana karbar magani a asibiti.
Daya daga cikin mutanen da suka zo daga garin Gwozan ya bayyana damuwarsu. Yace sun shiga wani hali a garinsu inda ana karkashesu. A kofar sarkin garin Gwozan 'yan Boko Haram sun kafa tutarsu domin babu jami'an tsaro. Bugu da kari babu wanda ya kawo masu tallafi. Sun gayawa gwamna amma ya gargadesu kada su gayawa 'yan jarida domin jami'an tsaro na aikinsu.
Kwamishanan 'yansandan jihar Bornon Lawal Tanko ya ziyarci gidan gwamnati inda ya ba mutanen hakuri kuma an kwace bindigar dake hannun dansandan da ya harbi Bello an kuma cire masa hula kana aka tasa keyarsa gaba.
Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.