Mataimakin gwamnan jihar ta Borno Alhaji Zanna Umar Mustapha shi yayi kiran lokacin da ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira da suka fito daga garin na Gwoza zuwa wasu kauyuka dake makwaftaka da jihar Borno.
Mataimakin gwamnan ya shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa al'ummar garin Gwozan na cikin halin lahaula walakawati ganin cewa har yanzu 'yan Boko Haram ke rike da garin. Wadanda suka samu suka gudu wasu sun shiga garin Madagali wasu kuma suna Uba. Yace sun ga mutane cikin halin kunci lamarin da ya sa wasu ma suna kuka. Amma ya tabbatar cewa jami'an tsaro suna nan suna fafatawa da 'yanbindigan.
Mafi yawan 'yan gudun hijiran sun shiga garin Madagali ne dake jihar Adamawa. Gwamnatin jihar Bornon ta tura manyan motoci domin jigilar wadanda suka samu suka kubuta zuwa wasu wuraren dake da dan dama dama a jihar tare da sama masu kayan abinci da na kwanciya da na wanki.
Kawo yanzu ba'a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ba. Mataimakin gwamnan yace sanin wannan sai Allah. A garin yanzu mata ne ma ke yiwa wadanda aka kashe jana'iza. Ya sake kiran gwamnatin tarayya musamman shugaban kasa ya sake duba abubuwa ya kawo karshen tashin hankalin da kungiyar Boko Haram ta jefa kasar ciki.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.