Tun makon jiya 'yan Boko Haram suka fatattaki mutanen garin tare da kashe na kashewa. Babu maza a garin yanzu domin 'yan Boko Haram sun yi farautar duk wani namuji dake garin. Mata da basu iya gudu ba da yara kanana aka bari.
Yawancin al'ummar garin sun fice zuwa dazuzuka da hawan duwatsu inda suka samu suka tsere da rayukansu. Lamarin ne ya sa jami'an tsaro suka kara karfi da karfe domin kwato garin.
To amma wasu matsaloli sun kunno kai daga barikin sojoji dake cikin garin Maiduguri inda matan sojoji suka tada bori akan kin amincewa da tura mazajensu zuwa yakar 'yan kungiyar Boko Haram. A barikin Maimalari matan sun bazu kan hanya tare da kone tayoyi domin nuna kin amincewarsu da tura mazajensu bakin daga bisa dalilan cewa ana kashe masu mazajensu domin ba'a basu isassun kayan aiki.
Wani soja da ba'a bayyana sunasa ba yace sun fahimta cewa gwamnati ba da gaske ta keyi ba wajen yakar 'yan kungiyar. Yace a matsayinsu na sojojin Najeriya ashirye suke su gama da 'yan kungiyar amma ba'a basu isassun makamai. Sun jinjinawa matansu da jajircewar da su kayi akan yunkurin manyansu na son kwashesu zuwa wasu wuraren na daban. Idan sojoji sun samu yadda suke so ba zasu kwashe mako guda ba da zasu gama da maharan. Suna ganin akwai wata makarkashiya game da irin abun dake wakana.
A can garin Gwozan wani da yake fakewa cikin duwatsu yace har yanzu 'yan Boko Haram suna cikin garin kuma suna bi gida gida suna duba matan da suka rage. Yaran suma sun soma ciwon gudawa. Matan da yaransu suna fama da karancin abinci. Wadanda suka tsere zuwa garin Madagali su ma wasoson garin rogo su keyi.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.