Wasu sojoji daga shiyya to bakwai ta rundunar sojojin Nigeria sun kusa cikin ofishin ‘yan jarida nan ta Daily Trust, inda suka tafi da mai’aikatan jaridar su biyu domin amsawa babban Kwamandan sojojin na shiyyar. Babban edita na Daily Trust ya baiyana abin da ya faru da cewa, sojojin sun zo karkashin jagoranchin sabon mataimakin kakakin shiyyar, wato kanar Sani Usman wanda basu same shi a ofishinsa ba, don haka suka dauki ma’aikatan jaridar mutum biyu gaban shi kwamandan shiyyar, in da aka bukaci jaridar da ta janye wannan labarin. Babban editan Malam Hamza Idris yakare da cewa duk abin da suka rubuta da kuma kafofin da suka basu wannan labarin, suna matukar kokarinsu wajen ganin sun tabbatar da sahihancin labaran dakuma bawa kowa damar fadin nashi ‘bangaren.