Wadanda suka isa Mubi suna zaune ne a wata makaranta inda jama'ar Allah ke taimaka masu.
Malam Muhammed Cubaru Buba na hadakar majalisar musulmi a yankin Mubi yana cikin jami'an dake tallafawa 'yan gudun hijiran. Ya kuma bayyanawa wakilin Muryar Amurka cewa yawan 'ayn gudun hijiran na karuwa. Bugu da kari wasu mata kuma sai haifuwa suke yi. Yace suna basu daidai gwargwadon abun da jama'a ke kawowa kamar abubuwan da suka shafi abincinsu da wajen kwanciya da magani da dai sauransu.
Wadanda suka gane inda 'yanuwansu suke majalisar musulman tana taimaka masu da kudin mota domin su samu natsuwa.
Wata mace da ta haifu ita ma ta nuna godiya da abubuwan da ake yi masu.
Shi kuma Abdullahi Umar shugaban karamar hukumar Tongo yace yana da 'yan gudun hijira da dama a yankinsa wadanda suka hada da wasu daga jihar Taraba da rikicin kabilanci ya rabasu da gidajensu. Su ma ana taimaka masu da abinci. Sun samu nasarar sa wasu a gidajen 'yanuwansu wasu kuma an basu wuri suna zaune.
Alhaji Abubakar Abdullahi Sardaunan Michika na ganin akwai bukatar kai tallafi wa al'ummomin yankunan Madagali da Michika wanda su ma matsalar hare-haren 'yan bindiga ke shafa. Yace a gaggauta a yi anfani da kudaden da aka tara, gwamnati ta kafa kwamitoci ma garuruwan da abun ya shafa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.