Kanal Hamid Ali yace sai a yi kone-kone a kashe mutane a ce wai kungiyar Boko Haram ce tayi. Har yau har gobe babu wanda aka kama aka kaishi kotu balantana ma ayi masa hukunci domin a san abun dake faruwa. Idan an ce an kama mutane babu wanda zai sake jin abun da ya faru.
Dangane da ko yana da shakka akan ita kungiyar ta Boko Haram yace yana da shakka babba. Yace yayi imani cewa Boko Haram da Yusuf ya soma yau ba ita ce ba. Yace wadannan na yanzu an kirkirosu ne aka sa masu rigar Boko Haram suna yiwa arewa ta'adanci. Boko Haram din Yusuf 'yansanda suka fara yaka suka kuma ce suna son su kafa daula ta musulunci. Yace yaya za'a yi wanda yake son ya kafa daular musulunci kuma yana bin musulmai yana kashe su yana kona gidajensu. Shin idan sun kafa daular wanene zasu mulka bayan sun kashe musulman.
Kanal Ali yayi imani cewa akwai wata manufa a kasa. Yace tun da ake kashe mutane a jihohin arewa maso gabas shugaban kasa bai taba zuwa wurin ya zauna ko kuma ya yiwa mutane jaje ba. Amma da zara an dasa bam a Abuja zai fito a kafar telibijan ranar yayi magana.
Akan matakan da zasu dauka yace abu ne na tsaro sabili da haka ba zasu fito fili su bayyana abun da zasu yi ba. Sai dai mutane su kirkiro hanyoyin da zasu kare kawunansu. Kada su dogara ga 'yansanda ko sojoji. Sojojin da 'yansandan suna nan ana kashe mutane. Akwai zargin cewa su ma sojojin suna kashe mutane.
Ga karin bayani.