Rigingimun a yankin na arewa maso gabas sun yi kamari inda kwana kwanan nan 'yan kungiyar Boko Haram suka kwace Gwoza suka kafa tasu tutar bayan sun gallazawa jama'a da kone gidajensu da dukiyoyinsu har ma da sace wasu mutane.
Ministan makamashi Alhaji Muhammed Wakil shi ya wakilci shugaban kasa da uwargidansa a wurin bada tallafin na musamman. Ya bayyanawa manema labarai irin halin da ya ga jama'a da lamarin ya shafa da kuma irin bayanan da yayi masu.
Ministan yace sun je sun gansu kuma duk wanda ya ga halin da suke ciki hankalinsa zai tashi domin yanayin da suke ciki bashi da dadi musamman wadanda suke cikin makarantu. Zuwansa ya kawo masu farin ciki ganin irin kayan da suka kai masu. Sun kai kaya cikin tireloli shida da kudi domin a taimaka.
Yace zuwan nasa ba na siyasa ba ne. Abun da ya faru ka iya samun kowa. Shi kansa daga wurin ya fito. Idan an fara sake gina muhallan mutanen gwamnatin tarayya zata taimaka musamman tun da sojoji sun kwato karamar hukumar daga 'yan Boko Haram.
Ga karin bayani.