Yace sun fara fahimtar juna kuma wasu wurare da kabilar Tiv ta kauracewa mutanen sun fara komawa inda suka saba zama.
Kauyen da aka sace wani jirgin ruwa jami'an tsaro sun kubutar dashi tare da mutanen sai dai mace daya da ta rasu. Yanzu gwamnan ya girke sojoji talatin a wurin.
Akan zama da shugabannin al'umma da sarakuna mukaddashin gwamnan yace babu wanda basu zauna dashi ba domin a samo masalaha. Sun zauna da sarakuna da shugabannin addinai da shugabanin al'umma.
Yace da ya dawo daga umrah abun ya bata masa rai domin sai a ce an daidaita sai kuma wani rikicin ya barke dalili ke nan ya dauki wani mataki mai tsanani. Yayi masu kashedi yace duk wani basarake ko shugaban karamar hukuma da ya bari aka sake samun wata husuma to ya kuka da kansa domin za'a yi maganinsa. Tun da yayi wannan kashedin shi ma ya samu lafiya da kwanciyar rai.
Dangane da wai ba'a yiwa mutane hukunci lamarin da yasa kowa yana yin abun da ya ga dama sai mukaddashin gwamnan yace da idan abu ya faru ana bari 'yansandan wurin su yi hukunci amma yanzu ba haka ba ne. Da zara abu ya faru dole 'yansandan wurin su kai maganar hekwata inda za'a hada har da jami'an SSS domin yin bincike.
Ga karin bayani.