A daren Laraba ne a garin Azare dake cikin Jihar Bauchi, wasu boma-bomai da aka daura akan babura suka fashe.
Yayin da 'yan Najeriya ke dakun ganin gwamnatin tarayya ta cika alkawarinta na sasantawa da 'yan kungiyar Boko Haram da kuma kwato 'yan matan Chibok daga kungiyar, wasu suna tababan yarjejeniyar tsagaita wuta
Makon da ya wuce Danlami Ahmadu ya shaidawa wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa cewa kungiyarsa ta Boko Haram ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin tarayya a wani zama da suka yi a kasar Chadi. Daga baya ita ma gwamnatin ta tabbatar da hakan.
Wasu 'yan kungiyar Boko Haram sun yarda a sasanta, wasu kuma basu yarda ba.
Tun lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da zaman yin sulhu da kungiyar Boko Haram a kasar Chadi 'yan kasar musamman daga arewa maso gabas suka soma tofa albarkacin bakinsu.
Ana zaton yau ne wakilan gwamnatin tarayyar Najeriya da na kungiyar Boko Haram zasu zauna a teburin shawara yau a kasar Chadi.
Wasu 'yan Najeriya masu gudun hijira a kasar Kamaru ne suka furta kalaman
Duk da cewa 'yan kungiyar sun kai sabbin hare hare a jihar Barno, gwamnatin Njaeirya tace yarjejeniyar tananan daram.
Iyayen 'yan matan Chibok na shakku, da tababa da kuma taka tsan-tsan da labarin sulhun da aka yi da Boko Haram
Kotun Soja ta fara zamanta Alhamis kan Sojoji 97 da ya hada da wasu 16 da ake zargi da yin bore da kuma kin yin fada arewa maso gabacin kasar domin yakar masu tsassauran ra'ayin addini, makoni biyu bayan da aka yankewa wasu 12 hukuncin kisa ta harbi, domin bore da neman kashe Kwamandan su.
Ana tautaunawa kan sakin ‘yan matan Chibok sama 200 da’aka sa ce wata shida da suka shude dakuma ganin an sasanta kan hare-hare.
A cigaba da firar da abokin aiki yayi da Danladi Ahmadu na kungiyar Boko Haram ya tabo abubuwa da dama har da ikirarin tsagaita wuta da yakin da suke fafatawa da gwamnatin Najeriya
Domin Kari