An jima ana samun jama'a da dama da kan fito su bayyana kansu a matsayin 'yan kungiyar ta Boko Haram da kuma yin alkawarin tsagaita wuta amma daga baya sai a ji kamar ba'a taba yi ba.
Irin wadannan maharan sukan cigaba da bude wuta a duk inda suke so da kuma lokacin da suke so. To saidai a wannan karon lamarin ya dan banbanta sabili da shigowar kasashen dake makwaftaka da Najeriya wadanda su ma lamarin ya soma shafarsu.
Al'ummomin Borno da Adamawa da Yobe da rigingimun suka fi shafa suna cigaba da fatan a wannan lokacin batun zai zama gaskiya domin an sha irin wannan kwangaba kwanbayan. A da can bayan an zauna da wasu dake kiran kansu 'yan kungiyar Boko Haram sai Abubakar Shekau ya fito cikin faifan bidiyo yayi watsi da maganar yace ba da yawunsa aka yi ba.
Wani da aka zanta dashi yace a taron da suka yi a Chadi na farko wa ya wakilci jihohin Borno, Adamawa da Yobe? Babu wanda ya wakilci talakawa a cikin taron. Yace sun gaji ba "gafara sa ba kafo" domin akwa wani lokaci da aka ce an cimma yarjejeniya har mutane na murna amma kuma sai hare-hare suka kara kamari.
Wani yace Allah yasa an yi da gaskiya, babu yaudara. Ba zai zama taron biyan bukatan wasu ba kawai. Amma suna jiran gwamnansu ya fito yayi magana su san inda suka tsaya.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.