Tun bayan da aka bada sanarwar cewa an cimma sulhu tsakanin kungiyar Boko Haram da hukumomin Najeriya tare da taimakon kasashen Kamaru da Chadi, wanda ake kyautata zaton cewa watakila zai kai ga sako 'yan matan Chibok da aka sace tun a watan afrilu, sai dai ba duka 'yan Najeriya ba ne suka yarda da wannan labari, da yawan su na bayyana shakku da tababar cewa anya kuwa wannan batu gaskiya ne?
Daga cikin masu irin wannan ra'ayi na shakku da tababa akwai shugabannin al'ummar Chibok wadanda aka sacewa 'ya'ya. Shugaban al'ummar Chibok mazauna garin Abuja Tsambido Hosea Abana yayi cikakken bayani kan dalilan su na yin shakku da tababa a wata tattaunawa da babban editan Sashen Hausa Aliyu Mustapha Sokoto:
Game da wannan tababa da shakku da kuka ji al'ummar Chibok na bayyanawa game da cewa an cimma jituwar da ta kai ga sako musu 'ya'ya, Aliyu Mustapha Sokoto ya sake komawa ga wakilin Sashen Hausa Umar Farouk Musa wanda shi ne ya fara bada labarin sulhun duk duniya ta ji shi, har ma ya tattauna da wakilin kungiyar Boko Haram wanda ke cikin masu tattaunawar sulhun. Aliyu Mustaphan Sokoto ya tambayi Umar Farouk Musa ko me ya bambanta wannan yarjejeniyar sulhu da sauran wadanda aka kukkula a baya amma suka wargaje?
Babban editan Sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustaphan Sokoto ne ya tattauna da shugaban al'ummar Chibok mazauna garin Abuja Tsambido Hosea Abana da kuma Wakilin Sashen Hausa a Abuja Umar Farouk Musa.