Yau a kasar Chadi kamar yadda muka sanar makon jiya wakilan gwamnatin tarayya da wakilan kungiyar Boko Haram zasu zauna a kan teburin shawara.
Zasu yi zaman nasu ne a karkashin shugabancin shugaban kasar Chadi Idris Deby wanda tun farko ya shiga tsakanin kungiyar da kasar Kamaru har ya kaiga sakin wadanda kungiyar tayi garkuwa dasu. Idan ba'a manta ba kungiyar ta sace matar firayim ministan kasar Kamaru da wasu 'yan kasar China fiye da goma.
A zaman da suka yi makon jiya sun kaiga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta kodayake 'yan kungiyar sun kashe wasu a jihohin Borno da Adamawa cikin wannan makon. Amma hafsan hafsoshin Najeriya ya umurci sojojinsa su tsagaita wuta.
Mai magana da yawun gwamnatin Najeriya yace suna da karfin gwiwar cewa wadanda suka zauna dasu a Chadi makon da ya gabata na hannun daman shugaban kungiyar Boko Haram ne, wato Shekau, kuma mutane ne da suka san abun da suke yi.
Su 'yan Boko Haram suka nemi shugaban Chadi ya shiga tsakani lamarin da ya kara karfafa wakilan Najeriya ganin irin tasirin da shugaban Chadin yake dashi wurin 'yan kungiyar.