Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maganar Sasantawa da Boko Haram Siyasa ce Kawai


Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP
Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP

Yayin da 'yan Najeriya ke dakun ganin gwamnatin tarayya ta cika alkawarinta na sasantawa da 'yan kungiyar Boko Haram da kuma kwato 'yan matan Chibok daga kungiyar, wasu suna tababan yarjejeniyar tsagaita wuta

'Yan Najeriya na cigaba da bayyana tababansu game da batun sasantawa da kungiyar Boko Haram din.

Ibrahim Garba Wala shugaban kungiyar tuntubar juna ta arewa yace matsalar Boko Haram da tabarbarewar tsaro a arewa musamman arewa maso gabas, gwamnatin Najeriya ta sha fitowa tana cewa zata yi kaza ko kaza amma duk a banza. Babu kuma inda za'a ce gwamnati tayi kokari ko ta tabuka wani abun a zo a gani. Halin da gwamnati ta nuna ya gina shakku da kokwanto a zukatan mutane.

'Yan arewa maso gabas su ne suka sha fama domin haka babu wani abun da za'a fada yanzu da zai kwantar da hankalin mutane illa abun da aka gani a zahirance. Duk abun da ya shafi sojoji ko siyasa mutane basu yadda dashi ba.

Nasiru Ibrahim Darazo sakataren watsa labarai na kwamitin APC na jihar Bauchi yace alamarin dama siyasa ce. Dama can ya fada cewa idan zabe ya karato jam'iyyar PDP dake mulki a karkashin shugaban kasa zata yi yunkurin kawo karshen fitintinun domin a nunawa jama'a kokarin da gwamnati keyi. Duk wannan abun dodorido ne. Shati fadi ne ake yiwa talaka. Ta ina aka ga 'yan Boko Haram? Yaushe aka zauna dasu? Idan gwamnati tayi magana dasu me yasa bata fito ta bayyanawa duniya ba cewa ga yadda suka yi.

Akan 'yan matan Chibok idan da ana son a kubutar dasu tuntuni da an yi. Abu ne na siyasa da ake yiwa mutane. Sai da zabe ya karato domin su cimma burinsu na siyasa domin a zabesu nan gaba shi ne suke cewa an samu tsagaita wuta. Amma sai gashi an samu hare-hare har guda biyu. Sabili da haka maganar ta zama tamkar fira.

Tun can farko toshon mai baiwa shugaban kasa shawara akan tsaro Janaral Azazi ya fito yace PDP ita ce Boko Haram. Bai yi mako guda ba aka koreshi. Akwai zargin cewa tshon hafsan sojojin Najeriya da tsohon gwamnan Borno su ne suke taimakawa kungiyar Boko Haram. Sabo da haka yanzu mafita gwamnati ke nema.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG