An bude taron hafsan hafsoshin kasashen dake gabar tafkin Chadi, wato Najeriya, Nijar Kamaru, Chadi har da Benin a babban birnin Najeriya Abuja.
Wasu sun soma mayarda martani akan umurnin da shugaban kasa ya bayar cewa hedkwatar sojojin dake yaki da Boko Hara ta kwashe nata-i-nata ta koma Maiduguri.
Wakilin Sashen Hausa dake jihar Borno Haruna Dauda Biu ya tattauna da shugaban rundunar sojan Najeriya dake Borno.
Masana harkokin tsaro da al’amuran yau da kullum na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da batun wanda ke daukan nauyin kungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a arewacin Najeriya da wasu makwabtanta.
Masana harkoki diplomasiyya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai Jamhuriyar Nijar da Chadi.
Bayan wani hari da 'yan kunar bakin wake suka kai a Yola, babban birnin Jahar Adamawa, bayanai daga hukumomi na cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu na ci gaba da karuwa.
Wata kungiyar dake hankoron kare hakkokin bil’adama ta fadi cewa ‘yan Najeriya fiye da dubu 8 suka mutu sanadiyar kokarin da gwamanti ke yi na murkushe mayakan sa kai na boko haram.
Ana kyautata zaton ganawar da Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi da hafsoshin sojojin Najeriya ba zai rasa nasaba da harkokin tsaro ba.
Biyo bayan furucin shugaban kasa Muhammad Buhari mutanen Borno sun yi maraba da samun hedkwaar sojoji amma da wasu sharuda
Hotunan kunar bakin wake da wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kan wata kasuwa a Maiduguri babban birnin jihar Borno dake arewa mas gabashin Najeriya.
A wani sabon yunkurin kawo karshen aika-aikar kungiyar Boko Haram sabon shugaban kasa ya bada umurnin daga hedkwatar sojojin dake fafatawa da kungiyar daga Abuja zuwa Maiduguri.
Domin Kari