Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Ndume Ya Goyi Bayan Matakin Kawo Karshen Boko Haram


Sanata Ali Mohammed Ndume
Sanata Ali Mohammed Ndume

A wani sabon yunkurin kawo karshen aika-aikar kungiyar Boko Haram sabon shugaban kasa ya bada umurnin daga hedkwatar sojojin dake fafatawa da kungiyar daga Abuja zuwa Maiduguri.

Sanata Ali Ndume shi ne yake wakiltar kudancin jihar Borno a majalisar dattawan Najeriya.

A firar da ya yi da Muryar Amurka ya tabo abubuwa da dama musamman batun mayarda hedkwatar dakarun sojoji Maiduguri a jihar Borno saboda yakar Boko Haram. Yace yunkurin shugaban kasa abun yabo ne domin abun da suke fata ne suna kuma jira-inji Ali Ndume.

Girke manyan dakarun tsaro a Maiduguri zai taimaka matuka. Yin hakan zai kawo karshen tashin tashinar 'yan Boko Haram. Yace dama can matsalar ita ce masu yaki suna wuri daban masu bada umurni kuma suna wani wuri daban. Ya kwatanta lamarin da mara lafiya da likita. Idan mara lafiya da likita basa wuri daya ba za'a samu warkewa ba.

Dangane da cewa Sanata Ndume ya janye daga neman shugabancin majalisar dattawa domin wai shugaban kasa yana goyon bayan wani sai yace babu gaskiya a maganar. Yana neman kujerar kuma shugaban kasa bai goyi bayan kowa ba. Yace idan jam'iyya ta tsayarda shawara akan inda shugaban majalisar zai fito zasu bi umurnin.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

XS
SM
MD
LG