Wata kungiyar dake hankoron kare hakkokin bil’adama ta fadi cewa ‘yan Najeriya fiye da dubu 8 suka mutu sanadiyar kokarin da gwamanti ke yi na murkushe mayakan sa kai na boko haram.
Ana kyautata zaton ganawar da Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi da hafsoshin sojojin Najeriya ba zai rasa nasaba da harkokin tsaro ba.
Biyo bayan furucin shugaban kasa Muhammad Buhari mutanen Borno sun yi maraba da samun hedkwaar sojoji amma da wasu sharuda
Hotunan kunar bakin wake da wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kan wata kasuwa a Maiduguri babban birnin jihar Borno dake arewa mas gabashin Najeriya.
A wani sabon yunkurin kawo karshen aika-aikar kungiyar Boko Haram sabon shugaban kasa ya bada umurnin daga hedkwatar sojojin dake fafatawa da kungiyar daga Abuja zuwa Maiduguri.
A 'yan kwanakin nan, kungiyar Boko Haram mai ta da kayar baya a arewacin Najeriya na ta kai hare-hare a yankin, inda a daren jiya ma rahotanni ke cewa sun kai wani hari a garin Ngalda da ke jahar Yobe.
An kai wani sabon hari a Maiduguri, babban birnin jahar Borno, inda mutane da dama suka jikkata. Wannan shi ne hari na uku da ya auku a tsakanin kwana guda da yini daya.
Wasu bama bamai guda biyu sun fashe a wajen wani bikin aure a arewa maso gabashin Najeriya a yau Juma’a, ya kuma kashe mutane bakwai tare da raunata wasu da dama.
Gwamnatin jihar Borno ta sanar da sassauta dokar hana zirga zirga a jihar daga karfe shida na safe zuwa karfe bakwai na maraice, sabanin yadda yake a da, daga karfe shida zuwa karfe goma na dare, domin jama'a su sami walwala a ranar damokaradiya.
Yayinda yake ziyarara garuruwan da sojojin Najeriya suka kwato daga hannun 'yan Boko Haram ya yaba masu da irin namujin aikin da suka yi
An Kama Makamai Da Kudin Kasashen Waje Daga Hannun 'Yan Ta'addar Boko Haram Bayan An Fatattake Su Daga Dikwa.
Al'ummansu karamar hukumar Kalbalge a jihar Adamawa sama da dubu 40 suna bukatan taimako na gaggawa biyo bayan daidaita su da kungiyar Boko Haram tayi.
Domin Kari