Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa Ke Daukan Nauyin Kungiyar Boko Haram?


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

Masana harkokin tsaro da al’amuran yau da kullum na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da batun wanda ke daukan nauyin kungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a arewacin Najeriya da wasu makwabtanta.

A shekarar da ta gabata, wani mai shiga tsakani wajen sasanta rikicin kungiyar ta Boko dan asalin kasar Australia Stephen Davis ya zargi tsohon gwamnan jahar Borno Sanata Ali Modu Sheriff da cewa shi ya ke daukar nauyin kungiyar, zargin da tuni Sheriff din ya musa.

Sai dai Dr. Bawa Abdulahi Wase, mai sharhi kan al’amuran da suka shafi tsaro, ya ce ya kamata gwamnati ta binciki zargin na Davis domin a ganinsa akwai kamshin gaskiya a ciki.

“Misali an kama Muhammad Yusuf, sojoji suka kama shi, aka kawo shi wurin ‘yan sanda, shi da kan shi (Sheriff) ya ba da umurni ya ce a harbe su, bayan sun ce suna so su ganshi, wannan ba zargi mu ke ba, abu ne da muka tabbatar, in bashi da hanu menene ya sa ya yi abin da ya yi” Inji Dr. Wase.

Sai dai a cewar Alhaji Musa Shehu Musa Gabon, wanda ke sharhi kan harkokin siyasa, yana da kwarin gwiwa Shugaba Muhammadu Buhari na da kwarewa sosai domin a ganinsa batun Boko Haram akwai siyasa a ciki.

“Shi a matsayinsa na tsohon soja wanda ya kai matsayin janar, kuma a matsayinsa wanda ya yi yakin Biafra kuma a matsayinsa na wanda na wanda ya san lokacin yakin Mai ta Tsine, ya na da masaniyar yadda zai shawo kan wannan batu.” Inji Alhaji Musa.

Ya kara da cewa tun asali an yi sakaci wajen kin daukan yakin a matsayin yaki na kasa ba na jahar Borno ba.

Ga karin bayani a rahoton Abdulwahab daga Bauchi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG