Shugaban hukumar kiwon lafiya ta duniya ta (WHO) ya ce an samu labaran kamuwa da COVID-19 a fadin duniya a cikin makwanni hudu fiye da watanni shidan farkon da annobar ta barke.
Rundunar sojojin Isra’ila ta fada a yau Laraba cewa ta kai farmaki ta sama kan wasu wuraren Syria da Iran a Syria a matsayin maida martini kan ajiye ababen fashewa a bakin iyakar kasar da ke yankin tsaunin Golan a cewar Isra’ila.
Yayin da kasuwar mai ke cigaba da fuskantar kalubale a duniya, kasashen Afurka masu arzikin man fetur sun shiga wani babban taro a Janhuriyar Nijar na duba hanyoyin kare darajar albarkatun mansu.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce hukumar na, a ta bakinsa, “matukar damuwa” da yadda cutar coronavirus ke ta yaduwa, musamman ma a Turai da Amurka.
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa-da-kasa ya ce kwamitin zai dauki matakai don tabbatar da cewa an ba dukkan 'yan wasa da wadanda zasu halarci gasar wasannin riga kafin COVID-19 a watan Yulin shekarar 2021.
Yankin Navajo a Amurka ya sanya matakan kulle tsawon makonni 3 saboda karuwar yaduwar cutar COVID-19.
A cigaba da tabo wasu batutuwan tuna baya game da rayuwar marigayi tsohon Shugaban Ghana, JJ Rawlings, an dan tabo wasu halayyansa da su ka yi matukar banbanta shi da sauran shugabanni da kuma takaitaccen tarihinsa.
Akalla mutane uku sun ji rauni ranar Laraba lokacin da wani bam ya tashi a wurin bikin tunawa da ranar tsoffin sojoji da ‘yan kasashen waje suka halarta a makabartar da ba ta musulmi ba a garin Jiddah na Saudiyya, a cewar wata sanarwar da hukumomi suka fitar.
Shugabannin Kurdawa na Syria na bayyana kwarin gwiwa kan ci gaban goyon bayan Amurka ga dakarunsu biyo bayan nasarar da tsohon mataimakin Shugaba Joe Biden ya samu a zaben shugaban kasa na Amurka a makon da ya gabata.
Yayin da ake cigaba da bayyana farin cikin samun maganin corona mai ingancin kashi 90 cikin 100, kwararru sun ce a bi a hankali, kai a yi watsi da batun sanya takunkumin baki. Hangen Dala, ba shiga birni ba.
Harin da aka kai a Kabul shine na baya-baya a jerin kashe-kashen manyan jami'ai da wasu da aka auna da babban birnin ya fuskanta a 'yan makonnin nan.
A Bangaladash akalla mutane dubu hamsin suka fito kan titunan Dhaka, babban birnin kasar a yau Litinin, don nuna adawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya kare sukar Musulunci a matsayin ‘yancin bayyana ra’ayi.
Domin Kari