Yayin da duniya ke cigaba da nuna alhini game da rasuwar tsohon Shugaban Ghana JJ Rawlings, jiya Alhamis, tsohon jami’in tsare tsaren jam’iyyar NDC Baba Shariff, ya bada takaitaccen tarihin marigayin da kuma halinsa.
JJ Rawlings, wanda aka haife shi ranar 22 ga watan Yunin 1947, ya mutu ne a wani asibitin Accra babban birnin kasar Ghana ya na mai shekaru 73 a duniya.
Ya jagoranci juyin mulkin soji sau biyu a shekarar 1979 ciki har da kwace mulki da ya yi daga hannun soji ya mika ga farar hula kafin daga bisani ya jagoranci ‘yan siyasar kasar wajen kafa tsarin siyasa mai jam’iyyu da dama.
Marigayi Rawlings, wanda mahaifinsa wani baturen kasar Scotland ne, manomi kuma masanin kimiyyar harhada sinadarai da magunguna, mai suna James Ramsey John, Kuma mahaifiyarsa mutumiyar Ghana mai suna Victoria Agbotui, ya hallaka wasu tsoffin shugabannin kasar da janar janar na soji saboda jin hanci da rashawa. Hasali ma ya sa an bindige wani alkalin kotun kolin kasar a bainar jama’a bisa zargin rashin gaskiya.
Amma ana wa marigayin ganin mai matukar kishin kasa da kuma son adalci, gaskiya da rikon amana.
A wata hira da wakilin VOA Ridwan Abbas ya yi da Baba Shariff, ya ba da takaitaccen tarihin marigayin da kuma bayanin wasu halayyansa masu ban shawa'a:
Facebook Forum