Masu zanga-zangar sun bukaci a kauracewa kayayyakin Faransa, kuma sun yi kokarin yin tattaki zuwa ofishin jakadancin Faransa amma ‘yan sanda suka hana su.
Kasar Faransa muhimmiyar kasar huldar kasuwancin Bangladesh ce, kuma mai ba Bangladesh din tallafi sosai.
‘Yan sanda sun kiyasta cewa kimanin mutane dubu hamsin ne suka halarci zanga-zangar, amma wadanda suka shirya gangamin sun ce sama da mutane 100,000 ne suka hallara domin yin zanga-zangar.
Shugaba Macron, ya janyo zanga-zanga a kasashen Musulmai, ciki har da Bangladesh, a lokacin da ya ce Faransa ba za ta taba yin watsi da ‘yancinta na bayyana ra’ayi ta zane-zanen barkwanci ba.
Kalamansa na zuwa ne bayan da wani ya kashe tare da sare kan wani malamin makaranta mai suna Samuel Paty, a farkon watan Oktoba, wanda ya nuna wa dalibansa wani zanen barkwanci na Annabi Muhammadu wanda mujallar Charlie Hebdo da ke Paris ta wallafa.
Facebook Forum