Kasar Jamus na shirin sake sanya matakan takaita zirga-zirga karo na biyu, yayin da Koriya ta Kudu ke shirin bude karin cibiyoyin gwajin COVID-19 a birnin Seoul.
Yayin da kasashe ke amincewa da riga kafin coronavirus, ana ci gaba da samun bukatar gaggawa ta bada riga kafin yayin da kuma ake samun adadin tarihi na masu kamuwa da cutar da kuma mace-mace a kasashe da yawa.
Gidan talabijin din Iran da kamfanin dillancin labaran IRNA sun ce da safiyar Asabar 12 ga watan Disamba ne aka rataye Ruhullah Zam, dan shekara 47 a duniya. Sai dai rahotannin basu bada karin bayani.
'Yan Adawa sun kauracewa zaben majalisar dokokin Venezuela bayan da suka yi zargin an tafka magudi.
Rasha ta kaddamar da aikin bada maganin rigakafin coronavirus a jiya Asabar domin dakile yaduwa cutar dake saurin yaduwa fiye da kowace cuta a tarihi.
Shugaban hukumar kiwon lafiya ta WHO ya fada a jiya Juma’a cewa yanzu da aka samu maganin rigakafi, yakamata kasashe su fara bincike tare da shirin tinkarar annoba ta gaba.
Kasar Birtaniya ta bada amincewar gaggawa akan fara amfani da sabon riga kafin COVID-19 da babban kamfani Pfizer da ke Amurka ya hada.
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ya mutu bayan fama da matsalar bugun zuciya, a cewar mai magana da yawunsa.
A jiya Asabar daruruwan masu zanga zanga a Guatemala sun abka cikin wani bangaren ginin majalisar dokoki kasar yayin da ake kara kaimin zanga zangar kin jinin matakin shugaba Aljendro Giammattei da na majalisar a kan tabbatar da kasafin kudi da ya rage kason ilimi da na kiwon lafiya.
Kungiyar 'yan ta'addan IS ta dauki alhakin harin rokokin da aka kai babban birnin Afghanistan.
Domin Kari