‘Yan majalisar dokokin Indonesia sun kara ta da batun kudurin dokar da zai ta haramta amfani da barasa a kasar.
Hakan na faruwa ne yayin da ake samun yawaitar mace-mace sanadiyyar shan barasar da aka hada ba tare da an bi ka’ida ba.
Sai dai masu sukar wannan kuduri sun ce, haramta shan barasar baki daya, zai kara ta’azzara amfani da barasa mai hadari da aka hada ba bisa ka’ida ba.
Majalisar wakilan kasar dai ta saka wannan batu cikin muhimman batutuwan da za ta fi mayar da hankali akansu a shekara mai zuwa, karkashin tsarin da ke fayyace muhimman batutuwan da suka shafi kasa.
A shekarar 2015 aka fara gabatar da kudurin amma aka jingine shi yayin da ya fuskantar suka.