“Duk da kashedi na tsawon shekaru, kasashe da dama basu yi shirin tinkarar COVID-19 ba,” inji babban darektan WHO Tedros Adhanom Gebreyesus, yana fadawa taro na musamma a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya game da coronavirus. Ya ce “wasu kasashe da dama bisa kuskure sun dauka ingancin tsarin kiwon lafiyar su ka iya kare su daga cutar".
Ya ce kasashen da suka yi kokari a yaki wasu nau'ukan cutar coronavirus a baya kamar cutar nunfashi ta SARS da cutar MERS da wasu cututtuka masu yado, sun taka rawar gani a yaki da COVID-19.
WHO ta sha suka daga wasu kasashe a kan yanda ta yi riko batun labarin farko da aka samu daga lkasasr China a faron wannan shekara.
Shugaban Amurka Donald Trump shine wanda yafi cira muryar sa wurin sukar hukumar, kana a ranar 29 ga watan Mayu ya sanar da ficewar Amurka daga hukumar ta kiwon lafiyar duniya. Sai dai zababben shugaba Joe Biden ya ce zai sauya wannan mataki da zaran ya kama aiki a cikin watan Janairu.
Shugaban na hukumar WHO, ya nanata bukatar raba maganin rigakafin COVID-19 daidai-wadade tsakanin manyan kasashe masu arziki da matalauta, yana mai cewa kimiya ba batun sadaka bane amma bukata ce ta kowace kasa.
Ya gargadi kasashe da sauya tunani a kan bada muhimmanci da kuma yanda suke kallon tsarin kiwon lafiya, indai har suna son kaucewa fadawa cikin wata annoba.