Gidan talabijin din kasar Iran ya ce an kashe wani masanin kimiyyar kasar a wani hari da aka kai – mutumin da Isra’ila ta yi zargin shi ya jagoranci shirin kera makamin nukiliyar sojan Iran har zuwa lokacin da aka wargaza shi a farkon shekarun 2000 a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Isra’ila da kisan Mohsen Fakhrizadeh a ranar Juma'a.
Amma Isra'ila ta ki ta ki cewa komai kan kisan, Ko da yake, Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya taba ambatan sunan Fakhrizadeh a wani taron manema labarai.
Gidan Talabijin din kasar ya ce "wasu gungun 'yan ta'adda ne dauke da makamai" suka kai wa Fakhrizadeh hari.
Ya mutu a karamin asibitin bayan da likitoci da ma’aikatan lafiya suka kasa farfado da shi.