Sarauniyar Ingila Elizabeth, mai shekaru 95, ta kamu da COVID kuma tana fuskantar alamomin marasa tsanani duk da cewa ta karbi allurar rigakafin cutar biyu, amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a wannan makon, kamar yadda fadar Buckingham ta fada yau Lahadi.