A babban birnin Faransa da ke Paris, masu zanga-zangar - da yawa sun jajirce a waje cikin sanyi da ruwan sama a ranar Asabar, dauke da kwalayen da aka rubuta "Gaskiya", "Yanci" da kuma "ba ma son tilastawan rigakafi".
Wasu kuma sun soki kalaman Shugaba Emmanuel Macron, wanda ya haifar da cece-kuce a makon da ya gabata lokacin da ya ce yana son ya bata ran wa duk wadanda ba a yi musu allurar ba ta hanyar sanya rayuwarsu cikin matsainacin halin inda dole zai tilasta musu yin allurar daga baya.
Idan ba a manta ba, kwanakin baya da suka gabata Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce yana son sanya rayuwar yau da kullun ga mutanen da ba a yi musu allurar rigakafi a cikin kasar ba cikin wahala.
Macron ya ce "Ni ba wai ina son cin zarafin Faransawa ba ne amma duk da haka, wadanda ba a yi musu alluran rigakafi ba, ina so in bata musu rai," in ji shi a wata hira da aka buga ranar Talata a jaridar Faransa Le Parisien.
"Ba zan jefa waɗanda ba a yi musu allurar ba a kurkuku. Ba zan yi musu allurar da karfi ba. ... Zamu matsa lamba ne ga wadanda ba a yi musu allurar ba ta hanyar takaita hanyoyin da za su iya yin ayyukan zamantakewa ya zamana da wahala."
Masu zanga-zangar sun mayar da martani ta hanyar amfani da harshensa, suna cewa "Zamu bata masa rai".
Zanga-zangar ta zo ne yayin da Faransa ta sami fiye da mutane 300,000 da suka kamu da cutar ta COVID-19 a cikin kwana guda a ranar Juma'a kuma majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis ta amince da wani kudirin doka na gwamnati wanda zai bukaci mutane su tabbatar da cewa suna da cikakken rigakafin cutar corona kafin su iya cin abinci a gidanjen abinci, ko tafiya a cikin jiragen kasa da ke zirga-zirga cikin gari ko halartar abubuwan al'adu.
Ma'aikatar cikin gidan Faransa ta ce mutane 105,200 ne suka halarci zanga-zangar ta ranar Asabar a fadin Faransa, 18,000 daga cikinsu a babban birnin kasar Paris, inda 'yan sanda suka bayar da rahoton kama mutane 10 da kuma wasu jami'ai uku da suka samu raunuka.
A wani wurin kuma an kama mutane 24 da kuma wasu ‘yan sanda bakwai da suka samu rauni a cewar ma’aikatar.