Wani hari ta sama da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira a yankin Tigray na arewacin kasar Habasha ya kashe 'yan gudun hijirar Eritriya uku.
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ma’aikata ‘yan kasar China uku da ke aikin gina madatsar ruwa dake tsakiyar Najeriya, tare da kashe wasu ma’aikatan guda biyu 'yan Nigeria, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Alhamis.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a duniya ya karu da kashi 11 cikin 100 a makon da ya gabata idan aka kwatanta da satin da ya wuce, inda nahiyoyin Amurka ne aka fi samun karin.
Hugo Maradona, kanin Diego Maradona kuma tsohon dan wasan kwallon kafa ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 52.
Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Turai (NIDO-Europe), reshen Italiya, ta ce kimanin mutane miliyan 1.5 daga cikin miliyan 3 da suka yi wa rajista a Italiya na fama da karancin fasfo na Najeriya.
Likitoci a Isra'ila sun fara ba da kashi na hudu na rigakafin mai kara kuzari na COVID-19 a ranar Litinin a zaman wani bangare na binciken gwaji don tantance ko karin harbin na iya bunkasa karfin rigakafi daga cutar.
Karuwar yaduwar cutar coronavirus ya sa kasashen larabawa sun dakatar da Najeriya da sauran wasu kasashen Afirka zuwa kasashensu.
Hukumomin New Zealand na binciken wani mutum da aka yi wa allurar rigakafin Covid-19 har sau 10 a rana guda.
Hukumomin Saudiyya sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya saboda barkewar sabuwar nau’in COVID-19, Omicron.
A karon farko kwayar cutar Corona na neman haifar da takaddamar diflomasiyyasa tsakanin kasashen Afurka da wasu kasashe na nahiyar Turai.
Wani likitan hakori a Italiya na fuskantar yiwuwar tuhumar aikata laifuka bayan ƙoƙarin karɓar rigakafin cutar coronavirus a hannun jabun da aka yi da 'silicone' na roba.
Najeriya ta shiga jerin kasashe 12 a fadin duniya da aka samu bulluwar sabon nau’in cutar coronavirus da ake kira Omicron. Nau’in cutar da aka gano a kudancin nahiyar Afrika ya shigo Najeriya ne ta hanyar wasu matafiya biyu da suka zo kasar daga Afrika ta kudu.
Domin Kari