An kai harin ne kan Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi, wanda ya karbi ragamar shugabancin kungiyar a ranar 31 ga Oktoba, 2019, kwanaki kadan bayan mutuwar shugaba Abu Bakr al-Baghdadi a wani farmaki da Amurka ta kai a yankin.
Wannan farmakin ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar IS ke kokarin sake bullowa, tare da kai wasu hare-hare a yankin, ciki har da harin kwanaki 10 a karshen watan da ya gabata na kwace wani gidan yari.
Dakarun Amurka na musamman sun sauka ne a cikin jirage masu saukar ungulu tare da kai farmaki a wani gida a wani yanki da ke hannun ‘yan tawaye a Syria, inda suka shafe sa’o’i biyu suna artabu da ‘yan bindiga, kamar yadda shaidu suka bayyana. Mazauna yankin sun bayyana ci gaba da harbe-harbe da fashe-fashe da aka yi a garin na Atmeh da ke kusa da kan iyakar Turkiyya, yankin da ke da sansanonin 'yan gudun hijira daga yakin basasar Siriya. Masu bada bayani na farko sun ce an kashe akalla mutane 13 da suka hada da yara shida da mata hudu.