Makasudun wannan rangadi na Shugaba N’gnazio Cassis shine karfafa dadaddiyar huldar dake tsakanin Nijer da Switzerland tare da duba hanyoyin inganta ayyukan jinkai a kasar ta Nijer wace matsalolin tsaron da ake fama da ita a yankin Sahel suka jefa jama’arta cikin kuncin rayuwa kamar yadda ya bayyana a wani taron manema labarai na hadin guiwa jim kadan bayan kammala tantaunawar da ta hada tawagogin kasashen 2.
Ya ce mahimmancin wannan ziyara ta farko ya sa tawagar mu ta kunshi shugabanni 3 domin mu kara nuna girman hulda da dangantakar dake tsakanin mu inda kasar mu ta shafe shekaru 44 ta na tallafawa a ayyukan ci gaba wuya da dadi.
Sannan muna yabawa ci gaban da aka samu a fannin dimokradiya inda a karon farko shugaban farar hula ya damka mulki a hannun wani zababben shugaba a bara.
A wuni na 2 na wannan rangadi shugaban tarayyar Switzerland N’gnazio Cassis da kakakin majlisar kasarsa da shugaban kungiyar agaji ta Red Cross za su ziyarci jihar Maradi kafin ya isa jihar Agadez a wuni na 3 na karshe inda zasu ganewa idanuwansu zahirin halin da jama’a ke ciki a karkara.
Shugaba Mohamed Bazoum mai masaukin baki ya yaba da wannan ziyara.
Ya ce an yi katari kun zo ne a wani lokacin da muke fuskantar manyan kalubale 2 wato matsalar tsaro da kuma matsalar karancin abinci sakamakon sakamakon gardamar damanar da ta gabata.
"Muna bukatar agajin gaugawa kamar yadda muka zayyana a tsarin bukatun agajin gaugawar da muka fara aiwatarwa da dan abinda ke hannun mu to amma girman wannan matsala ya sa muke fatan samun gudunmowar abokan hulda". A cewar shugaban.
Mataimakin kakakin majalisar dokokin kasa Kalla Hankouaro dake daya daga cikin jami’an tawagar Nijer na da kwarin gwiwar cewa al’umar wannan kasa za ta amfana da huldar dake tsakanin kasashen nan 2.
A gobe laraba ne shugaban tarayyar Switzerland N’gnazio Cassis ke kammala wannan rangadi da ake bayyanawa a matsayin na farko da wani mai rike da ragamar kasar ke gudanarwa a jamhuriyar Nijer .
Saurari rahoton Souley Mummuni Barma cikin sauti: