Wani kwale-kwalen kamun kifi da ke dauke da bakin haure masu yunkurin isa Turai ya kife a ranar Laraba a gabar tekun Girka, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.
An yanke wa wata mata ‘yar shekaru 44 hukuncin daurin shekaru sama da biyu a gidan yari a kasar Ingila ranar litinin, bisa samun ta da laifin zubar da ciki kimanin watanni takwas da daukar cikin.
Tsohon Firaministan Italiya wanda aka yi ta takaddama da shi, Silvio Berlusconi, ya mutu yana da shekaru 86 da haihuwa a duniya.
Wani mutum ya daba wa yara da manya biyu wuka a wani wurin shakatawa da safiyar ranar Alhamis, a wani hari da Macron ya ce ya girgiza kasar.
Jami'an Amurka da ke da alhakin bin diddigin kungiyar IS na ganin alamu masu ban tsoro da ke nuna cewa babban jagoran kungiyar ta'addancin yana karfafa ikonsa, a kan hanyar sadarwa ta duniya duk da dimbin hasarar da suka samu.
Hayakin da ke fitowa daga gobarar daji a kasar Canada ya kwarara har zuwa Gabashi da Yammacin tsakiyar Amurka a ranar Laraba, ya mamaye manyan biranen kasashen biyu a cikin wani yanayi mai muni.
Jam’iyyun hamayya a jamhuriyar Nijar sun dukufa wajen tayar da magoya bayansu daga barci don ganin sun yi nasara a zaben mutanen da za su wakilci ‘yan kasar mazauna kasashen waje a majalisar dokokin Nijar.
Shugabannin kasashen duniya da ke yaki da sauyin yanayi sun yi wani taro a birnin Bonn na kasar Jamus, domin bude matakin karshe na nazarin shekaru biyu kan ci gaban da aka samu na takaita gurbatar yanayi a duniya.
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa za ta sake bude ofisoshin diflomasiyya a kasar Saudiyya a cikin wannan mako, tare da maido da huldar diflomasiyya bayan da aka shafe shekaru bakwai ana takaddama a kai, kamar yadda kafar yada labarai ta kasar ta rawaito a ranar Litinin.
Majalisar Dinkin Duniya ta nada Dr. Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya Afirka (AfDB) da wasu shugabanni 21 da su jagoranci yaki da matsalar karancin abinci mai gina jiki a kowane nau'i a matsayin mambobi na kungiyar Scaling Up Nutrition (SUN) Movement Lead Group.
Fitaccen mawakin Najeriya, Damini Ebunoluwa Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy, ya kafa tarihin zama mawakin Afirka na farko da ya sayar da tikitin filin wasa na London mai daukan mutum 80,000.
Hauhawar farashin kayayyaki a duniya da yawan basussuka da yakin Ukraine, da kuma jinkirin murmurewa daga annobar COVID-19 sun sa kasashe masu tasowa fuskantar karancin guraben aikin yi don tallafa wa al'ummarsu, in ji wani rahoto daga kungiyar. Kungiyar Kwadago ta Duniya ko ILO a takaice.
Domin Kari