Yayin da Ghana ta kammala mataki na biyu na bunkasa samar da makamashin nukiliya, gwamnatin Amurka da Japan sun kara jaddada alkawarin tallafa wa shirin makamashin nukiliyar Ghana, da ke da nufin ba da ingantaccen makamashi mai tsabta.
Wata girgizar kasa mai karfi ta afku a gabashin kasar Japan a yammacin ranar Juma’a, kamar yadda kafar yada labarai ta NHK ta bayyana.
Turner ta rasu ranar Talata, bayan doguwar jinya a gidanta dake Küsnacht kusa da Zurich, a cewar manajanta. Ta zama 'yar kasar Switzerland ne shekaru goma da suka wuce.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ci tarar Meta, babban kamfanin da ya mallaki Facebook, dala biliyan 1.3 tare da umartarsa da ya daina mika bayanan masu amfani da shafin zuwa Amurka nan da watan Oktoba.
Shugabannin kasashen Larabawa na shirin halartar taron kungiyar kasashen Larabawa da za a yi ranar Juma'a a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, ciki har da shugaban kasar Syria a karon farko cikin shekaru sama da goma.
Birtaniya ta yi kira da a yi wa kotun Turai garambawul, bayan da alkalan da ke can suka hana zirga-zirgar jiragen da ke dauke da masu neman mafaka zuwa kasar Rwanda domin a tantance su a can.
Prigozhin wanda ya kasance makusancin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, a fili, ya yi barazanar janye mayakansa daga yankin Bakhmut, inda suke kan gaba wajen farmakin da Rasha take kaiwa, har sai dai idan sun samu makaman da suke bukata.
Ta yiwu a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Turkiyya da aka gudanar a jiya Lahadi bayan da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda ya kwashe shekaru 20 yana mulkin kasar, ya kasa samun cikakkiyar nasara akan babban abokin karawarsa a zaben.
Isra'ila da kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Falasdinu a zirin Gaza sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da yammacin Asabar, domin kawo karshen arangamar da aka shafe kwanaki biyar ana yi, wadda ta kuma yi sanadin mutuwar Falasdinawa 33 da suka hada da kananan yara da kuma mutane biyu a Isra'ila.
Kotu ta umurci Tsohon shugaban Amurka Donald ya biya matar da aka tabbatar ya yi ci zarafinta ta hanyar neman yin lalata da ita shekaru da dama da suka wuce, lamarin da Trump ya sha musantawa a baya.
Shugabannin kasashe, sarakuna da sarauniyoyi 90 daga sassan duniya suka halarci bikin wanda aka yi a Westminster Abbey.
Babu wani shugaban Amurk da ya taba halartar bikin nadin sarauta a Birtaniya.
Domin Kari