Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Nada Shugaban Bankin Raya Afirka Dr. Akinwumi A Sabon Mukami 


Dr. Akinwumi Adesina
Dr. Akinwumi Adesina

Majalisar Dinkin Duniya ta nada Dr. Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya Afirka (AfDB) da wasu shugabanni 21 da su jagoranci yaki da matsalar karancin abinci mai gina jiki a kowane nau'i a matsayin mambobi na kungiyar Scaling Up Nutrition (SUN) Movement Lead Group.

WASHINGTON, D.C. - Da yake magana a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni, Adesina ya ce yana matukar murna da wannan girmamwa ta nadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a yunkurin kawo karshen matsalar karancin abinci mai gina jiki a duniya.

Kungiyar ta SUN Movement wadda tsohon Sakatare-Janar Ban Ki-Moon ya kaddamar a shekarar 2010, ta na ci gaba da aikinta na inganta abinci mai gina jiki ne a duniya, karkashin jagorancin wasu fitattun mutane 22 da aka nada a duniya.

Wadannan mutane masu kima sun sadaukar da kansu wajen yaki da rashin abinci mai gina jiki a duk fadin duniya, da ayyuka bisa ka’idoji na mambobin kungiyar Jagorancin SUN.

Tare da nadin na baya-bayan nan, wadannan jiga-jigan masu fada a ji sun himmatu wajen bayar da shawarwarin samar da abinci mai gina jiki da kuma jagoranci kungiyar SUN don cimma burinta na kawar da duk wani nau’in rashin abinci mai gina jiki nan da shekarar 2030.

Haka kuma an nada wasu ‘yan Najeriya biyu tare da shugaban bankin na AfDB, mataimakin shugaban Islamic Development Bank wato bankin ci gaban Musulunci, Mansur Muhtar, da kuma shugaban zartarwa, Sahel Consulting Agriculture and Nutrition, Ndidi Nwuneli.

XS
SM
MD
LG