Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Macron Ya Ziyarci Wadanda Aka Kai Wa Hari Da Wuka Da Ya Girgiza Faransa


Shugaba Emmanuel Macron
Shugaba Emmanuel Macron

Wani mutum ya daba wa yara da manya biyu wuka a wani wurin shakatawa da safiyar ranar Alhamis, a wani hari da Macron ya ce ya girgiza kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, mai samun rakiyar matarsa, Brigitte, ya isa French Alps yau Juamma’a don ya kasance da iyalan mutanen da aka daba ma wuka jiya Alhmis a wani wurin shakatawa na gefen tafki da ke birnin Annecy.

Macron da matarsa sun fara yada zango ne a wani asibiti da ke birnin Grenoble, inda ake jinyar uku daga cikin yara hudun da aka daba ma wuka.

Macron da matarsa
Macron da matarsa

Jami’an gwamnati sun ce an yi tiyata ma duka yara hudun kuma jami’an jinya na kan sa ido kan halin da su ke ciki, inda daya daga cikin yaran ke cikin wani mawuyacin hali.

Ana kan jinyar yaro na hudu a birin Geneva, kasar Switzerland.

Zuwa yanzu dai ba a san ko Shugaban kasa da matarsa za su tafi Geneva din ba.

Wani mutum ne ya daba wuka ma yaran da wusa manyan biyu a wurin shakatawar da safiyar ranar Alhamis, a harin da Shugaba Macron ya ce ya girgiza kasar

Jagorar masu gabatar da kara, Line Bonnet-Mathis, ta ce dukka yaran hudu sun samu raunuka masu barazana ga rayukansu sanadiyyar daba masu wukar. Mai gabatar da karar ta ce karamin cikin yaran dan watanni 22 ne, biyu ‘yan shekaru 2 ne, sai kuma babban mai shekara 3.

Harin Wuka Na Faransa
Harin Wuka Na Faransa

Nan da nan 'yan sanda su ka kama wanda ake zargin, dan kasar Siriya mai shekaru 31. Firai ministar Faransa Elisabeth Borne ta ce wanda ake zargin yana da matsayin dan gudun hijira a kasar Sweden.

Shugaba Macron ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “Al’ummar kasa na cikin kaduwa.” Ya bayyana al'amarin a matsayin hari irin na "matsoraci.”

Wani faifan bidiyo mai nuna yadda harin ya faru yana ta yawo a shafukan sada zumunta. A cikin bidiyon, wani mutum sanye da bakin tabarau ya rufe kansa da shudin mayafi yana rike da wuka yayin da mutane ke kururuwar neman taimako.

Wata mata ta yi kokarin kare kanta daga maharin a wurin shakatawar da ke kewaye, amma ba ta iya hana shi jingina da abin hawanta ba, kana ya caccaka mata wuka.

Harin Wuka Na Faransa
Harin Wuka Na Faransa

Biyu daga cikin yaran da abun ya rutsa da su ‘yan Faransa ne. sauran biyun kuma ‘yan yawan bude ido ne, daya dan Birtaniya, da kuma dayan dan kasar Holland.

A birnin Paris, ‘yan majalisa sun tsayar da wata muhawara domin yin shiru na dan lokaci saboda wadanda abin ya shafa.

XS
SM
MD
LG