Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Tsarin Tantance Ci Gaban Da Aka Samu Na Yaki Da Sauyin Yanayi A Duniya


FILE - Sauyin Yanayi
FILE - Sauyin Yanayi

Shugabannin kasashen duniya da ke yaki da sauyin yanayi sun yi wani taro a birnin Bonn na kasar Jamus, domin bude matakin karshe na nazarin shekaru biyu kan ci gaban da aka samu na takaita gurbatar yanayi a duniya.

Taron sauyin yanayi na shekara-shekara na Bonn wani bangare ne na tsarin da kasashen duniya ke tantance irin ci gaban da aka samu wajen mutunta yarjejeniyar Paris ta 2015, kokarin duniya na hana yanayin zafi a duniya sama da digiri 1.5 a ma'aunin celcius.

Sakataran Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi Simon Stiell, a cikin wata sanarwa ya ce. "Wannan atisaye ne da aka yi niyya don tabbatar da cewa kowanne bangare ya ci gaba da gudanar da alkawarin da ya dauka, tare da sanin inda aka dosa da kuma yadda za a hanzarta matsawa don cimma manufofin yarjejeniyar Paris."

Duk da haka, Stiell ya yi gargadin cewa binciken zai kasance mai ma'ana ne kawai idan har an dauki matakan da suka dace.

Tsarin da ke kwashe shekaru biyu na faruwa sau daya a kowacce shekaru biyar, kamar yadda yarjejeniyar Paris ta tsara. Yana da sassa uku: tsarin tattara bayanai da lokacin shirye-shirye, kima na fasaha da kuma la'akari da abubuwan da tsarin ya haifar.

Za a kammala hada-hadar shirin ne a watan Nuwamba, lokacin da ake gudanar da taron sauyin yanayi na Amurka (COP28) na shekara-shekara a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG