Dakarun Najeriya sun gwabza da 'yan bindiga yau a Tungar Daji da ke karamar hukumar Anka jihar Zamfara lamarin da yayi sanadin mutuwar jami'an Soji biyu. An yi nasarar kawar da 'yan bindigan su 21 tare da raunata wasu da dama. An kuma karbe makamai da harassait.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo's ya kai ziyara cibiyar bincike ta kimiyya da fasaha ta matasa da ke Abuja, inda ya tattauna da su kan dogaro da kai.
Kungiyoyin fararen hula a jihar Damagaram dake Nijar sun gabatar da adu'o'i don neman mafita daga dokar da aka sanyawa kasafin kudin kasar na shekarar 2018
Kungiyoyin fararen hula da wasu jam'iyun siyasa na Damagaram sun gudanar da taron manema labarai
Dagewar gwamnatin tarayyar Najeriya akan maida hankali ga noma ta soma kawowa kasar albarka. Baicin fadada aikin noman shinkafa da aka gani a jihar Kebbi, yanzu a jihar Borno har dalarta an gani
Kasar Niger ta bi sahun sauran kasashen kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma wato UEMOA wajen anfani da banki daya asusu daya.
Domin Kari