A yau 4 ga watan Afrilu ne zagayowar shekaru 50 da kashe jagoran kwato hakkin bakar fatan Amurka.
Shekaru 50 Da Kashe Martin Luther King Jr

1
1965 - Martin Luther King, Jr. a lokacin da yake jawabi a garin Selma, Jihar Alabama ran 12 Fabrairu, 1965. King yayi gwagwarmaya da jami'in tsaro na Selma, watau Sherrif, Jim Clark, game da batun 'yancin jefa kuri'a da rajistar bakake a zaman masu jefa kuri'a a Selma.

2
1956 - A ranar 23 Fabrairu 1956, Martin Luther King, Jr., tare da Rev. Ralph D. Abernathy sun mika kawunansu ga jami'in 'yan sanda Lt. D.H. Lackey a Montgomery, Jihar Alabama, bayan da aka tuhume su da haddasa yamutsi dangane da gangamin kauracewa shiga bas-bas na birnin.

3
1956 - Mai dakin Martin Luther King, Jr., Coretta, tana masa marhabin bayan da ya fito kotu a birnin Montgomery ta Jihar Alabama ranar 22 Maris, 1956. Kotu ta same shi da laifin shirya gangamin kauracewa shiga bas-bas na birnin a saboda yadda ake ce bakaken fata sai a baya zasu zauna, turawa kuma a gaba.

4
1962 - Wasu malaman addini daga jihohin arewa su na tafa ma shugaban majalisar shugabannin coci-coci na jihohin kudu,m Martin Luther King Jr. a lokacin da yake jawabi cikin wata majami'a a Albany, Jihar Georgia a ranar 28 Agusta, 1962.
Facebook Forum