Akalla mutane 50 ne aka kashe tare da yin garkuwa da wasu da ba a tantance adadinsu ba, da suka hada da mata da kananan yara, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Yargoje da ke arewa maso yammacin Najeriya a karshen mako, kamar yadda mazauna garin suka bayyana a ranar Litinin.