Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Amnesty Ta Zargi Sojojin Najeriya Da Cin Zarafin Wasu Mata Da Suka Gudu Daga Hannun ‘Yan Boko Haram


Wasu mata da ‘yan mata da suka tsere daga mayakan Boko Haram
Wasu mata da ‘yan mata da suka tsere daga mayakan Boko Haram

A wani sabon rahoto da ta fidda, kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana cewa an tsare mata da ‘yan mata ba bisa ka'ida ba an kuma ci zarafinsu a cibiyoyin tsare mutane na sojojin Najeriya bayan da suka tsere daga hannun mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Rahoton ya ce an tsare wasu daga cikin matan tare da ‘ya’yansu tsawon shekaru saboda kawai zargin suna da alaka da kungiyar masu tsattsauran ra’ayin. Kungiyar Amnesty ta ambaci hirarraki 126, galibi da wadanda suka tsira daga wannan mummunan yanayin, a cikin shekaru 14 da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islaman suka kwashe suna kaddamar da hare-hare.

Rahoton ya sake bayyana damauwa akan keta hakkokin bil’adama da aka zargi sojojin Najeriya da yi, wadanda a baya aka zarge su da aikata hukuncin kisa na wuce gona da iri da kuma yin kame ba bisa ka’ida ba, a daya daga cikin rikice-rikice mafi dadewa da aka gani a duniya.

Ko da yake, rahoton ya lura cewa dabi’ar tsare mutane ba bisa ka'ida ba na tsawon lokaci bai bazu ba a cikin 'yan shekarun nan.

Rundunar sojan Najeriya ta yi watsi da rahoton a matsayin “mara tushe” kuma ta nanata cewa ta samu ci gaba wajen inganta kare hakkokin bil'adama kuma tana hukunta jami’anta da suka yi ba daidai ba.

Amma yanayin da wasu matan suka tsinci kansu a ciki bayan da suka tsere daga hannun ‘yan boko haram na da matukar muni, lamarin da ya sa wasunsu suka gwammace su koma wa ‘yan Boko Haram, abin da Niki Frederiek, mai bincike kan rikice-rikice na kungiyar Amnesty International, ya fada kenan game da cibiyoyin da ake tsare mutane a sansanonin soja da ke jihar Borno.

Rahoton ya ce akalla mutane 31 da suka tsira da aka yi hira da su sun ce an tsare su ba bisa ka’ida ba a cibiyoyin, abin da ke nuna cewa wannan dabi’ar ta bazu.

"Dole ne hukumomin Najeriya su tallafa wa wadannan 'yan mata da mata yayin da suka koma cikin al'umma," in ji Samira Daoud, daraktar kungiyar Amnesty International a yammaci da tsakiyar Afirka.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG