Kungiyar Tarrayar Turai ba asusun tallafawa kanananan yara- UNICEF naira biliyan tara domin kula da harkokin lafiya, ruwa da tsabtace muhalli a jihohin Plateau, Ekiti, Adamawa da kuma Kebbi.
Tsohuwar ministar harkokin matar a Najeriya ta ce tilas a daura damarar kara wayarwa da jama'a kai dpomin su fahimci dimbin amfanin rigakafin cutar ta Polio
Gwamnatin jihar Jigawa tayi wa kananan yara sama da miliyan daya rigakafin cutar kyanda, a cikin ayyukan makon lafiya na 2013 da aka yi a jihar
A bayan da aka samu wata matsala a yankin Tarauni, an roki al'ummar Jihar Kano da kada su yarda da masu yada jita-jitar cewa maganin rigakafin Polio ya lalace
Matar gwamnan jihar Lagos, Mrs. Abimbola Fashola, tayi kira ga sauran kungiyoyi dake sashen lafiya a kasa gaba daya, da su taimaka wajen rage mutuwar kananan yara
An shawarci mata a jihar Osun, su dauki kwararan matakai domin kiyaye ‘ya’yansu daga kamuwa da zazzabin cizon sauro
Wani sabon bincike a kan yadda ake jinyar cutar zazzabin cizon sauro da sida (HIV /AIDS) a Nigeriya ya nuna cewa, kashi 53% na wadanda suka kamu da cututukan ne suke jinyar kansu
Dr. Lawal Aliyu Rabe, darektan Kiwon lafiya daga tushe a Jihar Katsina, yayi bayanin yadda a Hausance aka samu kalmar rigakafi da kuma dalilin da ake yinsa.
Wani bincike da aka wallafa a wata wadda take bayyana yunkurin da ake yi a tsakanin al’umma da kuma tsare tsare ta wajen maida hankali kan gidajen da suka fi fuskantar hatsari, ta bayyana cewa, wannan yunkurin zai iya zama da amfani a yunkurin kare kananan yara daga zama a gidajen dake da hadari.
‘Yan majalisar dokoki na jihar Bauchi suna kokarin fito da wata doka, wadda ta zama dole ga masu yin aure suje asibiti domin gwajin cutar kanjamau.
Za a yi amfani da wannan kudi ta hannun hukumar Kiwon lafiya ta Duniya domin sanya idanu da binciken wuraren da ake samun yaduwar cutar a Najeriya
Kungiyar masu fama da cutar Polio ta Najeriya ta roki iyaye da su yi wa Allah su kai 'ya'yansu a ba su maganin hana kamuwa da wannan cuta mai janyo nakkasa
Domin Kari