Da yake karbar wani rahoto kan wannan aiki a yankin karamar hukumar Tarauni, jagoran kwamitin yaki da cutar Polio a Jihar Kano, kuma mataimakin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yace ba za su zuba ido kawai su koma gefe su na kyale ma'aikatan da aka dora wa amanar gudanar da aikin su na yin abinda suka ga dama.
Yana magana ne kan yadda aka bar wasu na'urorin sanyaya maganin, watau Firij, babu wuta jikinsu a Tarauni, alhalin da wannan magani yake bukatar a koyaushe a bar shi cikin sanyi. Sai dai Dr. Ganduje yace wannan bai kai ga lalacewar maganin ba.
Wakiliyarmu ta kiwon lafiya, Baraka Bashir, ta aiko da cikakken bayani kan wannan lamari daga Kano...