Bisa ga bayanin dake dauke da rattaba hannun Alh. Mati Ali, an yiwa makon lakabi “mata masu shayarwa, da jarirai domin lafiyarsu.”
Ali yace, anyi wannan rigakafin a wurare dari biya da saba’in da shida a jihar. Ya kara da cewa, an shirya za’a yiwa yara fiye da miliyan daya rigakafin, an taimaki kananan yara dubu 956,169 da abincin gina jiki.
Bisa ga cewashi an kuma yiwa mata 92, 961 bayani kan shayar da mama da tsabtar wurin zamansu. Yace, “Fiye da ma’aikata 3,000 ne suka taimaka a wannan aikin. Aikin ya samu ne ta wurin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ma’aikatar lafiya ta kasa (NPHDA).
Ya kara cewa, an dauki wannan matakin ne domin rage mutuwar kananan yara, kariyar cutar kyanda da sauran cututtuka dake kashe kananan yara, da kuma inganta aiki a wannan fannin.