Likita Katrina Korfmacher, darektar shirin ayyuka tsakanin al’umma ta asibitin jami’ar Rochester da ake kira “Community Outreach and Engagement” (URMC), tace “An jima da daukar gubar dalmaa a matsayin matsalar da za a iya magancewa daga gidaje”, saboda haka injita, yana da muhimmanci jama’a su fahimci abinda ake bukata da suyi, domin a rage yaduwar wannan hadari.
Dokokin Amurka sun dauki gubar dalma a matsayin abinda yafi kowanne hatsari ga yara a muhalli, saboda haka aka hana amfani da dalma a man fetir cikin shekarar 1976, aka kuma hana amfani da ita a fenti a shekarar 1978 domin rage illar cutar da kuma hanyoyin yada ta. Sau da dama ana daukar cutar da gubar dalma ke sawa ne ta wurin amfani da kura, fenti da kuma kasar da take da kewayen gida, kamin a hana amfani da fenti da akayi da dalma.
Bincike ya nuna cewa, kananan yara da aka fi samun cutar a jininsu suna zaune ne a gidajen talakawa, aka kuma tarar cewa, kimanin kashi 19% ma gidajen Amurka suna fuskantar barazanar gubar dalma, wannan adadin ya karu zuwa kashi 35% tsakanin gidajen talakawa. An gina kimanin kashi 86% ma gidajen Rochester ne kafin gwamnatin tarayya ta kafa dokar hana amfani da dalma.
Binciken Magani ya nuna cewa gubar dalma tana da illa ga lafiyar da hanyoyin koyo da kuma rayuwar mutum musamman kananan yara, dalili ken an da ake kara sa ido da maida hankali domin tabbatar da kare muhalli da gidajen da kanannan yara suke zama.