Dr. Rabe yace ana ce "rigakafi" ne domin bayyana wanda ya riga yin kafi a tsakanin cutar da kuma magani, domin wadansu cututtukan su na da wuyar yin magani idan sun riga yin kafi a jikin mutum.
Kwararren likitan, wanda yayi magana a zauren taron yaki da cutar Polio da Muryar amurka ta gudanar kwanakin baya a garin Katsina, yace yawancin ana yin rigakafin ne domin cututtuka irinsu shan inna ko Polio, watau cututtukan da kwayar cuta mai suna Virus take haddasawa.
Amma kuma yace akwai wasu cututtukan da wasu kwayoyin cutar ma suke haddasawa, kamar cutar nan ta tarin fuka wadda yace ita ba Virus ce ke haddasawa ba.
Ga cikakken bayanin da kwararren likita Dr. lawal Aliyu Rabe yayi game da salsalar kalmar "Rigakafi" da dimbin amfanin yin hakan.