Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya baiyyana damuwar shi cewa Nijeriya tayi baya wajen maganar lafiya ta duniya baki daya.
Likitoci sun gano kwayar cutar Ebola a kasar Guinea, lokacin da wata irin zazzafar masassara mai sa zubar jini ta fatar jiki ta barke ta kuma halaka mutane 34 a kalla a kasar.
A shekaru uku masu zuwa, kamfanin hada magunguna na AstraZeneca, zai sa jarin Naira miliyan 48 a binciken magunguna a Nijeriya domin ya gina yawan magunguna da kuma taimakon masana yin bincike.
Jami’an lafiya daga ma’aikatar lafiya na jihar Kebbi suna binciken mutuwar dalibai guda uku na makarantar sakandire ta Kanta a karamar hukumar Argungu, ta jihar Kebbi.
Gwamnatin tarayya tace karuwar jarirai da ake haifa da kwayar cutar kanjamau ya zama kalubale ga ‘yan Nijeriya.
Kwamishinar kiwon lafiya ta jihar ta ce duk da tashin hankalin 'yan Boko Haram a jihar, ana samun ci gaba a harkokin kula da lafiyar jama'a.
Nasarar da ake samu akan yaki da zazzabin cizon sauro ya bar hatsarin kamuwa da cutar mafi yawa ga kasashen Afrika 10, in ji wani bincike da Lancet Medical Journal ta buga.
Masana ilimin kimiyya sun ce sun gano abun da suke jin cewa kwayar halittar gado ce mai kwakkwarar alaka da kiba fiye da kima.
Ganin cewa jihar Abia ita ce ta 8 cikin jihohin dake da yawan cutar kanjamau a Nijeriya, kwamishinan lafiyar jihar, Dr. Okechukwu Ogar yayi kira domin rage yaduwar cutar a jihar.
Masu bincike na Amurka da Birtaniya sun yi harsashen cewa, yana yiwuwa dumamar yanayi ta haifar da cutar malariya dake kisa a wuraren da ba a saba da samun cutar ba.
Kwamishinan kiwon lafiya, Dr. Abubakar Tafida, yace gwamnati zata ci gaba da kokarin tabbatar da cewa ba a samu bullar shan inna a jihar ba.
A jihar Bauchi, wata hukumar da ke yaki da cututukar da dama ta horar da ma'aikatan jinya domin su sami kwarewa wajen gano cutar zazzabin cizon sauro da wuri in mararlafiya ya je asibiti.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.