Dr. Abdulaziz Mohamed Manga, shugaban wanan hukumar ya bayana cewa dole ne a san dalilin ciwon mutum kafin a bashi magani idan ya zo da cuta. Ya ce, "Ba za ka bada magani ga mutum ba sai ka tabatar da menene ke kawo masa wanan cutar."
Dr. Manga ya fadi cewa cututuka da yawa sukan kawo ciwon kai da zazzabi, ba cutar cizon sauro kadai ba. Sabo da haka, ya kamata a tabatar da irin Cutar da mutum ke dauke da ita kafin a bada magani.
Ya kara da cewa, ana bukatar koyar da maikatan jinya sosai domin sanin yadda ya kamata a yi wanan binciken ciwon marasa lafiya kafin su bada magani. Ya ce idan aka cigaba da ba da magani ba da cikakken sanin cutar da ke cikin jiki ba, za a iya sa jiki ya daina jin magani, ko kuma zazzabin malaria ya dena jin magani ba.
Dr. Manga ya ce sunyi ma wa maikatan duka baban asibitocin dake Jihar Bauchi horon nan. Ya kuma ce suna da shiri musaman domin kananan asibitoci domin suna da yawa.
Ga wakiliyar mu Amina Abdulahi Girbo da cikaken labarin.