A cikin bayanin da suka yi a wata mujallar ayyukan kimiyya, masu binciken sun ce sun gano cewa, cutar malariya tafi yawa a shekarun da aka yi zafi fiye da shekarun da yanayi yake da sanyi-sanyi.
Suka ce idan duniya ta ci gaba da kara dumama, mutanen da suke zaune a wurare masu zafi zasu fi shiga cikin hadari sabili da basu da kariya daga cutar.
Hukumar lafiya ta duniya tace zazzabin cizon sauro yana kashe sama da mutane dubu dari shida kowacce shekara, lamarin da yafi muni a nahiyar Afrika.
Sauro ne yake yada cutar malariya, ana kuma iya kare kamuwa da cutar ta wajen amfani da maganin sauro ku kwana a gidan sauro ko kuma shan magani.