Direkta kungiyar yaki da cutar kanjamau (NACA) Prof John Idoko yace rage yawan yaran da ake haifa da cutar kanjamau yana kara zama da wahala yayinda mata suna kara kin yarda su haihu a gidajen shan magani inda ake samun kayan aikin hana bada cutar kanjamau daga uwa zuwa da.
Wannan ya zo ne daidai lokacin da wadanda abin ya shafa suke tattaunawa game da yadda zasu tabbatar da yin amfani da shirin kawas da yaduwar Uwa zuwa Da na wannan cutar, cikin fadin kasar.
Majalisar dinkin duniya ta ce Nijeriya ita ce kasar da aka fi samun yawan jariran da ake haihuwa da kwayar cutar kanjamau.
Shugaban kungiyar NACA ya nuna cewa ko da yake shirye shiryen kare yaduwar uwa zuwa da na cutar kanjamau na nan ko ina, mata basu zuwa domin su ci moriyar wannan shirin.
A fadar shi, tun daga ranar kanjamau ta duniya ta 2009, kasar Nijeriya tana fama da aiwatar da aiyyukan kare jarirai daga kamuwa da kanjamau sai dai kuma akwai gibi da dole ne sai an cika shi tukunna.
Yace: "Idan ka yi maganin kamuwar jarirai a Nigeriya, ka yi maganinsa a dukan duniya kuma na tabbatar zamu iya yin maganinsa.”
Shugaban na NACA yace bincike kan yadda za’a aiwatar da wannan zai iya tallafawa kamar yadda za’a iya gani a shirn ceton rayukan mutane miliyoyin guda na gwamnatin tarayya.
Sai dai kuma yace masu binciken sunfi yawa a sashin bayarwa fiye da sashin karba, “matsalar yanzu ita ce yadda zamu motsa sashin karba.”