Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar kimiyya ta Nature, ya nuna cewa nauyin beran da ba a yiwa barbara da kwayar halittar gadon mai suna IRX-3 ba, ya ragu da kimanin kashi talatin cikin dari kasa da na beran da aka yiwa barbara da kwayar halittar gadon.
Berayen duka biyu sun ci abinci iri daya kuma sun motsa jiki daidai da juna. Amma sai aka gano cewa ramammen beran ba ya kamuwa da cutar sukari kuma jikin shi ba ya rike kitse.
Masanan masu bincike sun ce 'yan Adam su na da irin wannan kwayar halittar gado, kuma suka ce sakamakon binciken da suka yi na iya kaiwa ga samar da maganin kiba fiye da kima, da kuma cutar sukari, wadda wani lokaci cuta ce mai nasaba da kiba fiye da kima.
Masana ilimin kimiyyar jami'ar Chicago ne suka jagorancin binciken.
Kiba fiye da kima dai, babbar matsalar rashin lafiya ce da ake fama da ita a duka duniya, wadda ke kashe miliyoyin mutane a kowace shekara. Cin abincin da bai da inganci da karancin motsa jiki na cikin manyan dalilan da ke kawo kiba fiye da kima, a wani lokacin kuma matsala ce da ake iya yin gadon ta.