Masanan kimiyya dake kokarin nemo maganin da zai warkar da cutar kanjamau sun ce koma bayan da aka samu wajen mutane biyun da ake tsammani sun warke daga kanjamau ya kara masu kaimi ne maimaikon ya karya masu gwiwa.
A yawancin sassan duniya, sauro na zuwa ne lokaci-lokaci. A wasu sassan kuma, sauro na dauke da munanan cututtuka kamar su zazzabin cizon sauro.
A shekarar 2013, cutar Polio ko shan Inna ba ta nakkasa ko da yaro guda ba a Jihar Katsina, in ji Dr. Lawal Rabe Aliyu, na hukumar kiwon lafiya matakin farko a jihar
An kafa kwamitin mai wakilai 7 domin tabbatar da nasarar matakin karshe da aka dauka na kawar da Polio har abada daga jihar Sokoto
Gwamnatin tarayya ta baiyyana karuwar kwayar cutar hepatitis a kasar Najeriya
Kungiyar kiwon lafiyar Najeriya zata kashe yawan kudi Naira miliyan 415 shekara mai zuwa domin kauda cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro.
Wani bincike daga kasar Greece ya nuna cewa yaran da aka basu nono har tsawon fiye da wata shida sun nuna kaifin kwakwalwa, iya amfani da harshe, da kuma motsa jiki lokacin da suke kan girma fiye da wadanda basu sami wannan shayarwas ba.
Wani sabon bincike ya karyata maganar da ake yi cewa cin kwayoyi dangin su gyaada yana da lahani ga yaron dake cikin ciki saboda haka masu ciki su gujewa cin su.
Masanan kimiyya na Amurka sun gano yadda HIV ke kauda shirin kariyar jiki na mutum wanda yake haifas da kanjamau.
Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya tana shirin ayyana kasar Indiya a zaman wadda ta samu nasarar kawar da cutar Polio, ta fita daga jerin Najeriya, Pakistan da Afghanistan.
Wani sabon yaki na neman samar da magunguna masu saukin kudi a kasashe masu tasowa yana nan yana shirin - a wannan lokacin, domin warkar da cutar hepatitis C - fiye da shekaru goma bayan yaki kan kudaden maganin kanjamau a Afirika.
Jihar Kaduna ta doshi kawar da cutar Polio baki daya a bayan da aka shafe shekarar 2013 ba tare da bullar wannan cutar ba
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.