Dr. Lawal Rabe Aliyu, na hukumar kiwon lafiya matakin farko a Jihar Katsina, yace ya zuwa lokacin taron da Muryar Amurka ta shirya kan yaki da Polio a jihar Katsina a cikin watan Disamba, babu yaro ko guda daya da cutar Polio ta nakkasa a jihar.
Jami'in yace duk da cewa an samu matsalar tsallake wasu yara a lokutan da aka gudanar da ayyukan bayar da rigakafi a cikin jihar, ma'aikatan kiwon lafiya na jihar sun yi kokari matuka na ganin an kawar da irin wannan matsala a gaba.
Ya yaba wa ma'aikatan na kiwon lafiya a saboda turjiyarsu da dagewar da suka yi domin ganin ba a bar kowa a baya ba.
Dr. Rabe Aliyu yace da iyaye zasu fahimci amfani da muhimmancin wannan rigakafin, su kalle shi da idon basira, yayi imanin cewa sune zasu rika bin jami'an kiwon lafiya su na rokon da a ba 'ya'yansu.
Yace zasu ci gaba da wannan kokari domin ganin cewa a sabuwar shekarar nan ta 2014 ba a samu koda yaro daya da zai kamu da cutar Polio a jihar ba.